Tesfaye Jifar

Tesfaye Jifar
Rayuwa
Haihuwa Habasha, 23 ga Afirilu, 1976 (48 shekaru)
ƙasa Habasha
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines marathon (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Tesfaye Jifar (Amharic:ተስፋዬ jifar) an haife shi a ranar 23 ga watan Afrilu, a shekarar 1976) ɗan ƙasar Habasha ne ɗan wasan tsere mai nisa (Long-distance runner)

Jifar ya lashe tseren gudun marathon na birnin New York a shekara ta 2001, lokacinsa na 2:07:43 ya tsaya a matsayin mai rike da tarihin course na tsawon shekaru goma. A wannan shekarar ya kasance na biyu a gasar Marathon Tokyo[1] kuma ya lashe tseren gudun marathon na Saint Silvester da aka gudanar a Brazil. A gasar Marathon Amsterdam a shekarar 1999 ya zama na biyu kuma ya karya tarihin Habasha da Belayneh Dinsamo ya rike. Lokacin Jifar na sa'o'i 2:06:49 ya kasance tarihin kansa.

Tesfaye Jifar wanda ya taba lashe lambar yabo sau uku a gasar tseren Half marathon ta duniya IAAF, ya lashe tagulla a shekarar 1999 da 2000 da azurfa a shekarar 2001.[2]

A gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a shekarar 2001 da aka yi a Edmonton Jifar ya zo na bakwai a tseren gudun marathon.

  1. Tesfaye Jifar (Äthiopien) Archived 2006-05-23 at the Wayback Machine
  2. Tesfaye Jifar at World Athletics

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne